Wauta ce Chelsea ta kori Mourinho - Ferguson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho na fama da kalubale a gasar wasannin bana

Tsohon kociyan Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce mamallakin Chelsea, Roman Abramovich, zai yi wauta idan ya kori Jose Mourinho daga aiki.

Chelsea wadda ta dauki kofin Premier bara, tana mataki na 14 a kan teburin Premier bana, kuma an doke ta wasanni takwas daga karawa 15 da ta yi a gasar.

Ana rade-radin cewar Chelsea za ta sallami Mourinho daga Stamford Bridge idan bai lashe wasanni biyu da zai buga a gaba ba.

Ferguson ya ce "Bai ga dalilin da za a sallami daya daga cikin fitattun mai horas da tamaula da ake da shi a duniya ba".

Ya kuma kara da cewar Abromovich ya sallami masu horar wa da dama a cikin shekaru 10, yana da tabbas cewa ya koyi darasin yin hakan.

Mourinho ya sake dawowa horas da Chelsea a karo na biyu a 2013, ya kuma dauki kofin Premier da kuma na Capital One Cup.