Rooney da Schneiderlin suna yin jinya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rooney bai buga wasan da United ta buga da West Ham ba a ranar Asabar

'Yan kwallon Manchester United, Wayne Rooney da Morgan Schneiderlin ba za su buga wasan da kungiyar za ta yi da Wolfsburg a gasar cin kofin zakarun Turai ba.

United ce za ta ziyarci Jamus domin buga wasa na karshe na cikin rukuni a ranar Talata, wadda take bukatar samun nasara a karawar domin kai wa wasan gaba a gasar.

Rooney mai shekara 30, yana yin jinyar wanda bai samu damar buga wasan Premier da United ta tashi canjaras da West Ham a ranar Asabar ba.

Shi kuwa Schneiderlin mai shekara 26, ya ji rauni ne a wasan da United ta yi da West Ham, wanda hakan ne ya sa ba zai samu damar zuwa Jamus din ba.

United tana makati na biyu a rukuni na biyu a gasar cin kofin zakarun Turan, wadda ta bai wa PSV Eindhoven tazarar maki daya kacal.

Haka kuma 'yan wasan United da suke yin jinya sun hada da Phil Jones da Marcos Rojo da kuma Ander Herrera.

Ga 'yan wasan da United za ta yi amfani da su a Jamus:

De Gea, Romero, Blind, Borthwick-Jackson, Darmian, McNair, Smalling, Varela, Carrick, Fellaini, Goss, Lingard, Mata, Pereira, Powell, Schweinsteiger, Young, Martial, Memphis.