Lanzini zai yi jinyar makonni shida

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lanzini ya haskaka a wasansu da Liverpool

Dan kwallon West Ham, Manuel Lanzini zai yi jinyar makonni shida saboda rauni a cinyarsa.

Dan wasan Argentina din mai shekaru 22, ya ji rauni ne a lokacin atisaye a ranar Asabar kafin wasansu da Manchester United da suka tashi babu ci.

Lanzini, yana West Ham ne a matsayin aro daga kungiyar Al Jazira ta Abu Dhabi, kuma ya zura kwallaye hudu a wasanni 12.

A yanzu haka kuma wani dan wasan Hammers din Victor Moses shi ma ya ji rauni har ya soma jinya.

Dan kwallon Nigeria din shekaru 24, an cire shi a wasansu da United da suka fafata a Old Trafford.