An fitar da United daga gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta kare ne a matsayi na uku da maki takwas a rukuni na biyun

An cire Manchester United daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana, bayan da Wolfsburg ta doke ta 3-2 a karawar da suka yi a ranar Talata.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Martial a minti na 10 da fara wasa, Wolfsburg ta farke kwallo ne ta hannun Aparecido Rodrigues sannan Vieirinha ya kara ta biyu.

United ta samu kwallo ta biyu ne bayan da Wolfsburg ta ci gida ta hannun dan wasanta Guilavogui, kuma minti biyu tsakani Aparecido Rodrigues ya ci United kwallo ta uku.

Wasa na biyu na rukunin FSV Eindhoven ce ta ci CSKA Moskva 2-1.

Kuma hakan ne ya sa Wolfsburg ta kai wasan zagayen gaba da maki 12, PSV Eindhoven ta yi ta biyu da maki 10.

Manchester United ta kammala ne a mataki na uku da maki takwas, yayin da CSKA Moskva ta hada maki hudu a matsayi na hudu.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

  • Paris St G 2 - 0 Shakt Donsk
  • Real Madrid 8 - 0 Malmö FF
  • VfL Wolfsburg 3 - 2 Man Utd
  • Man City 4 - 2 B M'gladbach
  • PSV Eindhoven 2 - 1 CSKA
  • Benfica 1 - 2 Atl Madrid
  • Galatasaray 1 - 1 FC Astana
  • Sevilla 1 - 0 Juventus