Arsenal ta kai wasan zagayen gaba a kofin Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar 14 ga watan Disamba za a raba jadawalin wasannin zagaye na biyu

Arsenal ta kai wasan zagayen gaba da kungiyoyi 16 za su fafata a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai bayan da ta ci Olympiacos 3-0 a ranar Laraba.

Olivier Giroud ne ya ci wa Arsenal kwallayen uku a karawar, inda ya fara cin ta farko a minti na 29 da fara wasa, ya kuma kara ta biyu da aka dawo daga hutu da kuma ta uku da bugun fenariti.

Hakan ne ya kuma sa Giroud din ya zama dan wasan Arsenal na hudu da ya ci kwallaye uku rigis a wasa daya, bayan Henry da Bendtner da kuma Welbeck.

Wasa na biyu na rukunin kuwa Bayern Munich 2-0 ta doke Dinamo Zagreb, hakan ne ya sa Munich ta jagoranci rukunin na shida da maki 15, sai Arsenal ta biyu da maki tara.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

  • Bayer Levkn 1 - 1 Barcelona
  • Chelsea 2 - 0 FC Porto
  • Valencia 0 - 2 Lyon
  • Roma 0 - 0 BATE Bor
  • Dinamo Zagreb 0 - 2 Bayern Mun
  • Dynamo Kiev 1 - 0 M'bi Tel-Aviv
  • KAA Gent 2 - 1 Zenit St P