Daniel Sturridge zai yi jinyar makonni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana mataki na takwas a kan teburin Premier

Dan wasan Liverpool, Daniel Sturridge, zai yi jinyar makonni, bayan da ya ji rauni a wasan Premier da suka kara da Newcastle a ranar Lahadi.

Newcasatle United ce ta samu nasara a kan Liverpool da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka yi.

Sturridge ya shiga karawar ce a St James Park bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, kuma tuni likitoci suka yi masa aiki.

Dan kwallon bai dade da dawowa ba daga doguwar jinyar da ya yi a ciwon gwiwar kafa da kuma a sawunsa.

Wasanni 18 Sturridge kacal ya buga wa Liverpool, sakamakon jerin raunin da ya dunga fama da yi a kakar bara.