Man United ta yi kokari fiye da bara - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption United tana mataki na hudu a kan teburin Premier bana

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal, ya ce hujjoji sun nuna cewar United ta yi kokari fiye da bara, duk da an cire ta daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.

United ta kasa kaiwa wasan zagayen gaba na kungiyoyi 16 da za su fafata a gasar, bayan da Wolsburg ta doke ta da ci 3-2 a ranar Talata.

Van Gaal ya ce kaiwa matakin wasannin cikin rukuni a gasar cin kofin zakarun Turai da taka rawa a Capital One Cup da kuma zama ta hudu a kan teburin Premier ya nuna yadda kungiyar ke samun ci gaba.

Ya kuma ce ba zai iya kare kansa na cewar an fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turan ba.

Van Gaal wanda ya maye gurbin David Moyes a watan Mayun 2014, ya jagoranci United buga gasar cin kofin Zakarun Turai, da mar da ta kasa samu a lokacin Moyes din.