Ronaldo ya kara kafa tarihi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo ya tabbata a matsayi gwarzo

Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a gasar zakarun Turai bayan da ya zura kwallaye 11 a zagayen farko na gasar.

Ya kafa tarihin ne a wasan da suka doke Malmo da ci takwas da nema inda ya zura kwallaye hudu.

A baya, Ronaldo na rike da tarihin ne tare da dan kwallon Brazil, Luiz Adriano inda kowannensu ke da kwallaye tara a zagayen farko na wannan gasar.

Dan kwallon Portugal din wanda kuma yake rike da kambun gwarzon dan kwallon duniya watau Ballon d'Or a yanzu shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a gasar zakarun Turai.

Sakamakon sauran wasannin gasar zakarun Turai:

  • Paris St G 2-0 Shakt Donsk
  • Real Madrid 8-0 Malmö FF
  • PSV Eindhoven 2-1 CSKA
  • VfL Wolfsburg 3-2 Man Utd
  • Benfica 1-2 Atl Madrid
  • Galatasaray 1-1 FC Astana
  • Man City 4-2 B M'gladbach
  • Sevilla 1-0 Juventus