Swansea City ta raba gari da Garry Monk

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Fabrairun 2014 ne Monk ya fara horas da Swansea

Swansea City ta raba gari da kociyanta Garry Monk, bayan da ya ci wasa daya kawai a karawa 11 da ya yi a gasar cin kofin Premier ta bana.

Monk mai shekara 36, ya zauna a Swansea shekara 11, farko a matsayin dan wasa sanan ya maye gurbin Micheal Laudrup a watan Fabrairun 2014 a matakin kociyanta.

A ranar Asabar ne Leicester ta doke Swansea 3-0, wanda hakan ya sa ta koma mataki na 15 a kan teburin Premier.

Swansea ta ci wasanni uku ta kuma buga canjaras a karawa biyar yayin da aka doke ta fafatawa bakwai daga wasannin Premier 15 da ta yi, tana kuma da maki 14.

A wata sanarwa da kungiyar ta bayar ta ce ta fara neman kociyan da zai maye gurbin Garry Monk din.