Mai yiwuwa FIFA ta dakatar da Saliyo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai yiwuwar dakatar da tawagar 'yan kwallon Saliyo

Akwai yiwuwar FIFA za ta dakatar da Saliyo daga shiga harkar wasan kwallon kafa ta duniya, kwanaki uku kacal bayan an amince wa kasar karbar bakuncin wasan kwallon kafa na kasa da kasa.

Hakan ya biyo bayan umarnin da Majalisar wasanni ta kasar wacce hukuma ce gwamnati ta bayar na rusa kwamitin zartarwa na hukumar kwallon kafa ta Saliyon.

Mataimakin ministan wasanni na Saliyo Ishmael Al Sankoh Conteh, ya shaida wa BBC cewa yana tababa in har FIFA za ta dau wannan mataki.

Ya ce, "Da mu da FIFA dukkanmu mun yarda da wani kwamiti mai mutane bakwai, kuma wannan kwamiti ya amince ba za a dau irin wannan mataki ba kuma ba ma tsammanin FIFA zata sauya magana."

A baya ma dai FIFA ta haramtawa wasu kasashe shiga harkar kwallon kafa ta duniya.