Faransa ta dakatar da Benzema

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin Benzema da son bata suna Valbuena.

Hukumar kwallon kafar Faransa ta dakatar da Karim Benzema daga tawagar kwallo kafa ta kasar.

Yana fuskantar tuhuma ne kan aikata mugayen laifuka saboda zarginsa da ake yi da yi wa abokin aikinsa barazanar bata suna da wani bidiyon lalata.

Jami'ai sun ce za a dakatar da Benzema har sai an daidaita kan lamarin.

Benzema dai ya yi watsi da tuhumar, ya kuma ce ba shi da wata alaka da wata tawagar wani gungun mutane wadanda ke kokarin bata sunan Mathieu Valbuena.