Matar Stephen Keshi ta mutu

Image caption Stepehn Keshi na cikin rudanin mutuwar mai dakinsa.

Wadansu kafofin yada labarai a Najeriya sun ambato tsohon Kociyan Super Eagles Stephen Keshi, yana tabbatar da mutuwar mai dakinsa, Kate, a Amurka.

Keshi ya ce matar tasa ta dade ba ta da lafiya amma bai taba tsammanin rashin lafiyar zai yi sanadin mutuwarta ba.

Rahotanni sun ce Keshi na cikin rudani a halin yanzu saboda yadda yake tsananin son matar.

Wata majiya ta ruwaito cewa Keshi ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar jana'izarta.