Ina da kwarin gwiwa — Mourinho

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mourinho ya ce har yanzu ba su fitar da rai ba.

Kociyan Chelsea Jose Mourinho yana son kulob dinsa ya zama cikin kulob-kulob hudu da za su kasance a saman tebirin Premier a kakar wasa ta bana.

Kulob din Chelsea dai yana tsaka mai wuya a bana, inda yake a mataki na 14, wato ke nan yana bukatar maki 14 idan yana son zama na hudu.

Sai dai Mourinho ya ce, "Muna fatan za mu kare a mataki na hudu. A lissafe hakan mai yiwuwa ne, kuma za mu gwada mu gani".

A ranar Litinin ne kulob din na Chelsea zai fafata da Leicester, wadanda suka bayar da mamaki saboda rawar da suke takawa a kakar wasa ta bana.