Yaya Toure ne gwarzon dan kwallon kafar BBC na 2015

Image caption Toure ne dan wasa daya kacal da ya lashe kyautar sau uku.

An zabi dan kasar Ivory Coast, Yaya Toure, a matsayin gwarzon dan kwallon kafar Afirka na BBC na shekarar 2015.

Yaya Toure, mai shekara 32, shi ne dan wasa guda daya rak da ya lashe gasar sau uku, ko da ya ke 'yan Najeriya Nwankwo Kanu da Jay-Jay Okocha sun lashe ta sau bibiyu.

Masu sha'war wasan kwallon kafa ne dai suka zabi dan wasan na Manchester City,, wanda a shekarar 2013, ya cinye gasar, bayan ya doke Yacine Brahimi, Pierre-Emerick Aubameyang, Andre Ayew da Sadio Mane.

Toure ya shaida wa BBC cewa: ""Ina matukar alfahari. Samun wannan kyuta daga wajen magoya baya na abu ne mai ban mamaki."

Biyu daga cikin 'yan wasan da suka fafata a takarar sun taba cin gasar.

'Yan wasan su ne, dan kasar Algeria, Brahimi, wanda ya zama gwarzon dan kwallon kafar BBC na shekarar 2014 da kuma takwaransa dan kasar Ghana, Ayew, wanda shi kuma ya lashe gasar a shekarar 2011.

Sau uku a jere dan kasar Gabon, Aubameyang, yana shiga jerin 'yan wasan da suka yi takarar, yayin da dan kasar Senegal, Mane, ya shiga takarar a karon farko.

Sau shida ana sanya Toure a jerin wadanda ke yin takarar, kuma a shekarar da ya lashe gasar ta biyu, ya taimaka har sai da kasarsa, Ivory Coast, ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Kazalika, Toure ne kyaftin lokacin da aka yi gasar cin kofin Afirka a kasar Equatorial Guinea, kuma shi ne ya zura kwallo ta farko a zagayen kusa da na karshe lokacin da suka doke Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da ci 3-1.

Shugabar fannin labarai da al'amuran yau da kullum ta Sashen Afirka na BBC na, Vera Kwakofi, ta ce: "Irin jagorancin da Yaya Toure yake yi wa tagawar kwallon kafar kasarsa da kuma kulob dinsa, abin koyi ne ga matasan 'yan wasan da ke son koyi da shi".

Ta kara da cewa: "Muna alfahari, a matsayinmu na BBC, da zuwanmu nan domin maimaita tarihi da masu sha'war dan kwallon a duk duniya ."