An raba jadawalin gasar cin kofin Turai ta 2016

Image caption A ranar 10 ga watan Yuni za a fara wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai a Faransa

Wales da Ingila za su kara a gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a shekara mai zuwa, bayan da aka raba jadawalin fara gasar a ranar Asabar.

Wales da Ingila da Rasha da kuma Slovekia ne aka saka a rukuni na biyu, bayan da rukuni na uku ya kunshi Ireland ta Arewa wadda za ta fara buga gasar a karon farko da Jamus da Poland da kuma Ukraine.

Jamhuriyar Ireland kuwa tana rukuni biyar ne da ya kunshi Belgium da Italiya da Sweeden, rukuni na farko kuwa yana dauke da Faransa da Romania da Albenia da kuma Switzerland.

Za a fara wasan farko na bude gasar ne tsakanin Faransa da Romani a ranar Juma'a 10 ga watan Yuni a filin wasa na Stade de France.

Ga yadda aka raba jadawalin gasar:

Rukunin A: France, Romania, Albania, Switzerland

Rukunin B: England, Russia, Wales, Slovakia

Rukunin C: Germany, Ukraine, Poland, Northern Ireland

Rukunin D: Spain, Czech Republic, Turkey, Croatia

Rukunin E: Belgium, Italy, Republic of Ireland, Sweden

Rukunin F: Portugal, Iceland, Austria, Hungary