Hukumar Fifa ta bai wa Saliyo wa'adi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An amincewa Saliyo ta karbi bakuncin wasan tamaulaka, bayan da aka ce babu cutar Ebola a kasar

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta bai wa Saliyo wa'adin dawo da hukumar kwallon kafar kasar da ta rusa.

Fifa, ta umurci Saliyo da ta dawo da mahukuntan kwallon kafar kasar aiki daga nan zuwa Laraba 16 ga watan Disamba, ko kuma a dakatar da ita daga shiga sabgar tamaula a duniya.

A ranar Alhamis ne hukumar wasanni ta kasar ta sanar da soke kwamitin amintattu na hukumar kwallon kafar kasar.

Hukumar wasannin Saliyo ta ce ta yi hakan ne, bayan da Isa Johnson, ta rusa kwamitin mutane bakwai da aka kafa domin zabo mutanen da za su halarci taron hukumar kwallon kafar kasar da za a yi.

Sai dai kuma Fifa ta ce hukumar kwallon kafa ta kasa mai cin gashin kanta ce, bai kamata gwamnati ta yi katsalanda cikin harkokinta ba.