Nigeria ta dauki kofin matasa 'yan kasa da shekara 23

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Nigeria ta taba lashe lambar zinare a kwallon kafa a wasanin Olympics da aka yi a 1996

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta lashe kofin matasa 'yan kasa da shekara 23 na Afirka, bayan da ta doke ta Algeria da ci 2-1 a ranar Asabar.

Nigeria ta fara cin kwallon daga bugun fenatiti a minti na 14 da fara wasa kuma Etebo Oghenekaro ya ci kwallon kuma shi ne ya ci ta biyu.

Algeria ta ci kwallonta tilo ne bayan da dan wasan Nigeria mai tsaron baya Oduduwa Segun Tope ya ci gida saura minti 15 a je hutun rabin lokaci.

Da wannan nasarar Nigeria za ta wakilci Afirka a gasar kwallon kafa a wasannin Olympics da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Ita ma Algeria ta samu gurbin da za ta wakilci Afirkan tare da Afirka ta Kudu wadda ta doke Senegal a wasan neman mataki na uku a gasar a bugun fenariti.