Ya kamata mu kara kaimi - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Bournemouth ce ta doke United 2-1 a gasar Premier wasan mako na 16 a ranar Asabar

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal, ya umarci 'yan wasansa da su kara kaimi su kuma ci wasanni uku a jere domin su samu damar lashe kofin Premier bana.

Doke United 2-1 da Bournemouth ta yi na nufin kungiyar ta ci wasanni biyu daga cikin guda bakwai da ta yi a gasar ta Premier.

Kuma United din tana mataki na hudu a kan teburi, inda Manchester City wacce ke kan teburin Premier a mataki na daya ta ba ta tazarar maki uku.

Van Gaal ya ce rashin nasara a wasanni biyu abin takaici ne, ya kuma kamata su saka hazaka a wasannin da suke yi domin dawo da tagomashinsu.

Kociyan ya kuma ce ya kamata United ta ci wasanni uku a jere, wanda hakan zai ba ta damar darewa saman teburin Premier bayan Kirsimeti.