Gasar Firimiyar Nigeria za ta yi fice - Dikko

Image caption A cikin watan Janairu ko kuma farkon Fabrairu za a fara gasar Firimiyar Nigeria ta badi

Shugaban hukumar gasar Firimiyar Nigeria, Shehu Dikko, ya ce suna ta shirye-shiryen yadda za su kara daga darajar gasar ta Nigeria.

Shehu ya shaidawa BBC cewar shiga kungiyar gasar wasanni ta duniya da suka yi zai kara musu haske kan yadda sauran kasashe musamman na Turai suka inganta wasanninsu.

Ya kuma kara da cewar ziyarar gani da ido da suka jagoranci shuwagabannin kungiyoyin kwallon kafa na jihohi zuwa Landan, zai kara inganta yadda za su gudanar da ayyukansu.

A makon da za mu shiga ne hukumar za ta gudanar da taron da za ta yi bitar gasar da aka kammala ta bana, da kuma tsayar da ranar da za a fara wasannin badi.

Enyimba ce ta lashe kofin Firimiyar bana kuma karo na bakwai da ta dauki kofin, inda ta fara dauka a shekarar 2001 da 2002 da 2003 da 2005 da 2007 da kuma 2010.

Nigeria da Kenya da Afirka ta Kudu ne suka shiga rukunin gasar kwallon kafa ta kwarrarru ta duniya, wadda ta kunshi gasar Premier da La Liga da Bundesliga da sauransu.