Watakila Hodgson ya tsawaita zama a Ingila

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ingila ta lashe wasanninta na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai

Watakila kociyan tawagar kwallon kafar Ingila, Roy Hodgson, zai ci gaba da horas da tawagar har zuwa shekara 2018, in ji babban jami'in hukumar kwallon Ingila Martin Gleen.

A shekarar 2012 ne Ingila ta dauko Hodgson, wanda yarjejeniyar da suka kulla a matsayin kociyanta za ta kare bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2016.

Glenn ya ce idan har kociyan ya taka rawar gani a gasar cin kofin nahiyar Turai, tabbas za su tsawaita zamansa da tawagar Ingila.

A ranar Asabar ce aka raba jadawalin buga gasar ta Turai, inda aka saka Ingila a rukuni na biyu da ya hada da Wales da Rasha da kuma Slovakia.

Za a fara wasan farko na bude gasar ne a Faransa tsakanin Faransa da Romani a ranar Juma'a 10 ga watan Yuni a filin wasa na Stade de France.