Giroud ya cancanci a kara ba shi martaba - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger ya ce Giroud yana bayar da gudunmawa a Arsenal

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce Olivier Giroud, ya cancanci a kara ba shi martaba, saboda yadda yake taka rawa a wasannin da Arsenal din ke yi.

Taka rawar gani da Arsenal ke yi ne ya sa kungiyar ta koma mataki na daya a kan teburin Premier, bayan da ta ci Aston Villa 2-0 a ranar Lahadi.

Giroud ne ya ci kwallon farko a bugun fenariti a Villa Park kuma kwallo ta 50 da ya zura a raga a gasar ta Premier.

Haka kuma shi ne ya ci kwallaye uku rigis a ragar Olympiakos, wanda hakan ya taimaka wa Arsenal ta kai wasan zagayen gaba na Gasar Zakarun Turai.

Giroud shi ne dan kwallon Arsenal na bakwai da ya ci wa Arsenal kwallaye 50 a gasar ta Premier.

Jumullar ya ci wa Gunners kwallaye 72 a wasannin 121 da ya buga mata wasanni, ciki har da karawa 37 da ba a fara wasa da shi ba.

Ya kuma koma wasa Emirates ne daga Montpellier kan kudi fam miliyan 12 a watan Yunin 2012.