Europa: Man United za ta kara da Midtjylland

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 18 ga watan Fabrairu za a fara kece raini a wasannin Gasar Europa

Manchester United za ta fafata da Midtjylland a gasar kungiyoyi 32 da za su buga wasannin Europa League, bayan da aka cire ta daga Gasar Zakarun Turai.

Liverpool kuwa za ta kara ne da Augsburg, yayin da Tottenham za ta yi gumurzu da Fiorentina kuma karo na biyu kenan a jere da ake hada su buga gasar.

Valencia wadda Gary Neville ke horaswa za ta kece raini da Rapid Vienna.

Za su fara buga wasannin farko a tsakaninsu a ranar 18 ga watan Fabrairu, sannan su buga karawa ta biyu mako daya tsakani.

Ga jadawalin da aka raba na wasannin Europa League:

 • Valencia v Rapid Vienna
 • Fiorentina v Tottenham Hotspur
 • Borussia Dortmund v FC Porto
 • Fenerbahce v Lokomotiv Moscow
 • Anderlecht v Olympiakos
 • Midtjylland v Manchester United
 • Augsburg v Liverpool
 • Sparta Prague v Krasnodar
 • Galatasaray v Lazio
 • Sion v Braga
 • Shakhtar Donetsk v Schalke
 • Marseille v Athletic Bilbao
 • Sevilla v Molde
 • Sporting Lisbon v Bayer Leverkusen
 • Villarreal v Napoli
 • Saint-Etienne v Basel