Guardiola zai bayyana makomarsa a Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A shekarar 2013 Guardiola ya koma horas da Bayern Munich

Pep Guardiola ya ce a makon gobe ne zai fayyace idan zai ci gaba da horas da tamaula a Bayern Munich ko kuma akasin hakan.

Guardiola wanda ya jagoranci Munich lashe kofuna biyu tun komawarsa kungiyar a shekarar 2013, ana ta jita-jitar cewar zai koma kociyan Manchester City.

Kociyan ba zai amsa tambaya daga wajen yan jaridu kan sanin makomarsa a Jamus ba, amma kuma zai fitar da sanarwa bayan kammala hira da su.

Tun a ranar Laraba jaridar Marca ta wallafa cewar tuni Guardiola ya sanarwa da Bayern Munich cewar yana son barin kungiyar.

Munich tana mataki na daya a kan teburi, ta kuma bayar da tazarar maki biyar, za kuma ta buga wasanta na karshe a shekarar 2015 da Hannover a ranar Asabar.