Aguero zai dawo tamaula a karawa da Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Litinin ne Manchester City da Arsenal za su kara

Sergio Aguero zai dawo wasan tamaula a karawar da Manchester City za ta yi da Arsenal a gasar Premier wasan mako na 17 a ranar Litinin.

Aguero ya fara atisaye a City, bayan da ya yi jinyar da ta hana shi bugawa kungiyar wasanni hudu da ta yi a baya,

Dan wasan ya ji rauni ne a karawar da City ta ci Southampton 3-1 a gasar Premier da suka fafata a cikin watan Nuwamba.

Aguero wanda ya ci wa Manchester City kwallaye bakwai a gasar ta Premier, ya yi jinyar makonni shida.

Arsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier ta kuma bai wa Manchester City wadda take matsayi na uku tazarar maki daya kacal.