An nuna wasan kwallo kai tsaye a Somaliya

Image caption Kungiyar Al-shabaab dai ta umarci masu wasan kwallon kafa da su saka dogayen wanduna.

A karon farko an nuna wani wasan kwallon kafa kai tsaye a gidan tallabijin na kasar Somaliya.

A wasan, kungiyar rundunar sojin kasar ta Horseed ta doke ta 'yansanda Heegan da ci 2-1 a gasar cin kofin Janar Daud.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Somaliya Abdiqani Said Arab ya ce nuna wasan wani ci-gaba ne.

Kasar dai na murmurewa ne daga shekaru gommai da ta kwashe cikin rikici.

Karin bayani