Suarez ya ci kwallaye uku a wasa daya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona wadda ta lashe gasar a shekarun 2009 da 2011 na kokarin zama kungiya ta farko a duniya da ta lashe gasar sau uku.

Luis Suarez ya ci kwallaye uku a wasa daya domin bai wa kungiyarsa ta Barcelona damar kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi.

Suarez ya taka wannan rawar ganin ce duk da cewa Lionel Messi da Neymar ba su cikin wasan da Barcelona ta buga da kungiyar Guangzou, saboda raunukkan da suka samu.

A yanzu Barcelona za ta kara da kungiyar River Plate daga kasar Argentina a wasan karshe kuma idan kulob na Luis Enrique ya samu nasara, hakan na nufin ya lashe kofuna biyar a shekara ta 2015.

Barcelona ta lashe kofunan gasar La Liga da gasar zakarrun Turai da gasar Copa Del Rey da kuma Uefa Super Cup duk a wannan shekara.

Karin bayani