''Chelsea ba za ta bar rukunin Premier ba''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger dai ya tunkudi Mourinho lokacin da Chelsea ta doke Arsenal 2-0.

Arsene Wenger ya ce kungiyar Chelsea ba za ta fita daga rukunin gasar Premier ba duk da cewa suna matakin na 16 a teburin gasar.

Maki daya ne dai ya hana kulob din fadawa ajin kungiyoyin da za a fitar daga rukunin na zakarun wato relegation Zone.

''Suna cikin mawuyacin hali amma dai ba za su shiga cikin kungiyoyin da za a ragewa matsayi ba,'' in ji manajan na kulob din Arsenal.

Sai dai da aka tambaye shi ko yana jin mafita kawai ga Chelsea daga wannan halin shi ne ci gaba da aiki da Mourinho, sai Wenger ya ce, ''ba na son yin hasashe kan wasu abubuwa domin ba matsalata ba ce.''

Karin bayani