Bayern Munich ta bayar da tazarar maki takwas

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a kammala wasannin mako na 17 ranar Lahadi a gasar Bundesliga

Bayern Munich za ta shiga shekarar 2016 da tazarar maki takwas a kan teburin Bundesliga, bayan da ta doke Hannover da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar.

Bayern Munich ta samu fenariti ne bayan da Christian Schulz na Hannover ya taba kwallo da hannu, kuma Thomas Muller ne ya buga ya kuma ci wa Munich kwallon da ya ba ta maki uku a wasan.

Dan wasan Hannover, Leon Andreasen da kuma Robert Lewandowski na Bayern Munich dukkansu sun buga kwallo ta bugii turke a fafatawar.

Za a karasa wasannin mako na 17 a gasar Bundesliga tsakanin Hertha Berlin da Mainz 05 da na Borussia Monchengladbach da Darmstadt a ranar Lahadi.

Za a yi hutu a gasar Bundesliga a ranar Juma'a 22 ga watan Janairun 2016, za kuma a dawo yin gumurzu a wasannin mako na 18.