Chelsea ta nada Hiddink kociyan rikon kwarya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier da maki 15

Chelsea ta nada tsohon kocin Netherlands, Guus Hiddink, a matsayin mai horaswa na rikon kwarya zuwa karshen kakar wasan bana.

Hiddink ya maye gurbin Jose Mourinho wanda Chelsea ta sallama a ranar Alhamis, watanni bakwai bayan da ya lashe gasar Premier tare da kungiyar ta Chelsea.

Hiddink ya taba zama kocin riko a Chelsea inda ya lashe gasar FA a shekarar 2009.

Sabon koci Hiddink shi ne zai jagoranci kungiyar a gasar Premier da za ta buga da Sunderland a Stamford Bridge.

Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier da maki 15, bayan da ta yi wasanni 16 a gasar.