Barcelona ta lashe kofin zakarun nahiyoyi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Barcelona ta lashe kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyin duniya karo na uku kuma kofi na biyar da ta dauka a kakar wasan 2015.

Barcelona ta dauki kofin ne bayan da ta doke River Plate da ci 3-0, kuma Lionel Messi ne ya ci kwallon farko, sai Luis Suarez da ya ci biyu a karawar.

Suareze ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwallaye a raga, inda ya ci guda biyar a gasar, ciki har da guda uku rigis da ya ci Guangzhou Evergrande a wasan daf da karshe.

Barcelona ta zazzaga kwallaye 176 a wasannin bana, kuma shekarar da aka fi cin kwallaye a kungiyar kennan a tarihi, za kuma ta kara da Real Betis a wasan La Liga a ranar 30 ga watan Disamba.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga, kuma tana cikin kungiyoyin da za su buga wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da kuma Copa del Rey.