Madrid ta lallasa Rayo Vallecano da ci 10-2

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Real Madrid tana mataki na uku a kan teburin La Liga

Real Madrid ta casa Rayo Vallecano da ci 10-2 a gasar La Liga wasan mako na 16 da suka kara ranar Lahadi a Bernabeu.

'Yan wasan da suka ci wa Madrid kwallayen sun hada da Danilo da ya ci biyu da Bale wanda ya ci hudu, Benzema kuwa uku ya zura a raga sai Ronaldo da ya ci daya daga bugun fenariti.

Vallecano ta ci kwallaye biyu ne ta hannun Amaya da kuma Sanchez Ruiz, ta kuma kammala karawar da yan kwallo tara a fili, inda aka bai wa Roman Triguero da Baena jan kati.

Da wannan sakamakon Rel Madrid tana mataki na uku a kan teburi da maki 33, yayin da Atletico wadda ke matsayi na biyu za ta ziyarci Malaga a daren Lahadin.