Watford ta doke Liverpool da ci 3-0 a Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Watford ta koma mataki na bakwai a kan teburin Premier

Watford ta ci Liverpool 3-0 a gasar Premier wasan mako na 17 da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na dake kan titin Vicarage.

Golan Liverpool Adam Bogdan ne ya saki kwallon da ya kama, kuma nan take Nathan Ake ya samu damar da ya zura tamaula a raga.

Odion Igahlo ne ya ci ta biyu sannan ya kara ta uku bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon Watford ta koma mataki na bakwai da maki 28 a kan teburin Premier, yayin da Liverpool ta koma matsayi na tara da maki 24.

Watford za ta buga wasanta na gaba da Chelsea a Stamford Bridge, inda Liverpool kuwa za ta karbi bakuncin Leicester a Anfield.