Arsenal ta doke Manchester City da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal za ta ziyarci Southampton a ranar Asabar a wasan mako na 18

Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburin Premier, bayan da ta doke Manchester City da ci 2-1 a gasar mako na 17 da suka yi a ranar Litinin.

Theo Walcott ne ya fara ci wa Arsenal kwallon kuma ta 100 da ya zura a raga tun san da ya zama kwararren mai taka leda.

Olivier Giroud ne ya ci wa Arsenal kwallo ta biyu daf da za a je hutun rabin lokaci kuma ta 10 da ya ci a gasar Premier bana.

City ta zare kwallo daya ne ta hannun Yaya Toure saura minti takwas a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Arsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 36, yayin da Manchester City ke matsayi na uku da maki 32.

Arsenal za ta buga wasan mako na 18 da Southampton a filin wasa na St Mary, inda City za ta karbi bakuncin Sunderland a Ettihad a ranar Asabar.