An haramta wa Blatter da Platini shiga wasanni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi tsammanin Platini ne zai gaji Blatter.

Hukumar kwallon kafar duniya, Fifa ta haramtawa shugabanta Sepp Blatter da kuma shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, Michel Platini shiga dukkan wasu harkokin wasanni tsawon shekara takwas.

Hukumar ta dauki matakin ne bayan kwamitinta na da'a ya same su da laifin karbar hanci.

Haramcin zai fara aiki ne nan take.

Hakan dai na nufin, Blatter, mai shekara 79, ba zai sake shiga harkokin wasanni ba har abada.

Tun a shekarar 1998, Blatter ya fara shugabancin Fifa, ko da ya ke a kwanakin baya ya bayyana aniyarsa ta sauka daga shugabancin hukumar kafin zaben da za a yi a watan Fabrairu.

A baya dai an yi tsammanin Platini, mai shekara 60 ne zai gaji Blatter.

Sau uku Platini yana zama Zakaran kwallon kafar Turai, kuma shi ne tsohon kociyan kungiyar kwallon kafar Faransa, inda ya zama shugaban Uefa a shekarar 2007.

Blatter ya yi raddi

Sai dai a martani da ya yi bayan haramta masa shiga harkokin wasannin, Mista Blatter ya ce yana takaicin yadda aka mayar da shi "karkatacciyar bishiya mai dadin hawa" a fagen harkokin kwallon kafar duniya.

Ya kara da cewa hakan ya sa martabarsa ta zube, yana mai ce ya yi tsammanin ya gamsar da kwamitin da'a na Fifa a kan kalaman da ya yi cewa kudaden da ya bai wa Michel Platini na halaliya ne.

Mista Blatter ya ce ba zai taba yarda da hukuncin da aka yi masa ba, yana mai cewa nan gaba kadan zai daukaka kara.