Guardiola ya san kulob din da zai koma - Rummenigge

Hakkin mallakar hoto allsport
Image caption Ancelotti ne zai maye gurbin Guardiola a Bayern Munich

Shugaban Bayern Munich, Karl-Heinz Rummenigge, ya ce Pep Guardiola tuni ya zabi kungiyar da zai koma horaswa, bayan da ya amince zai bar su a karshen kakar bana.

A ranar Lahadi ne Bayern Munich ta sanar da cewar Pep Guardiola zai bar aikin horas da ita idan an kammala wasannin bana.

Ana kuma rade-radin cewa zai koma kociyan Manchester City ko Manchester United ko Chelsea ko kuma Arsenal.

Amma Rummenigge ya ce ya san kulob din da Gurdiola zai koma horas da tamaula, amma ba zai bayyana ba.

Tsohon kociyan Chelsea, Carlo Ancelotti, shi ne zai maye gurbin Gurdiola kuma tuni ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku da Munich.