United ta fi lalacewa lokacin Moyes - Phil Jones

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta koma matsayi na biyar a kan teburin Premier

Mai tsaron bayan Manchester United, Phil Jones, ya ce kungiyar ta fi lalacewa a loacin da David Moyes ya horas da 'yan wasanta.

United ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier, bayan da ta sha kashi a hannun Norwich da ci 2-1 a Old Trafford ranar Asabar.

Jones ya ce, "Bana jin cewar United ta gaza a yanzu, muna taka rawar gani fiye da wadda muka yi a lokacin David Moyes".

United ta kori Moyes a watan Afirilun 2014, bayan da ya yi aiki na watanni tara, kuma United ta kammala gasar Premier a mataki na bakwai a lokacin.

Louis van Gaal - wanda ya maye gurbin Moyes - ya kasa lashe wasanni shida da ya yi a jere, ciki har da wasan da aka cire United daga Gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana.