Del Bosque zai yi ritaya idan an gama gasar Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Del Bosque ya lashe kofin duniya da kuma na nahiyar Turai

Kociyan tawagar kwallon kafar Spaniya, Vicente del Bosque, na shirin yin ritaya daga aiki bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a 2016.

Del Bosque, mai shekara 64, ya jagoranci Spaniya domin lashe kofin duniya a shekarar 2010 da kuma na nahiyar Turai a shekarar 2012.

Kociyan ya ce, "Daf nake da yin ritaya, idan komai ya tafi kamar yadda ya kamata, bayan gasar kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa zan ajiye aiki na".

Ya kuma ce yana aiki ne karkashin hukumar kwallon kafar Spaniya, saboda haka zai tattauna da su kafin ya yanke shawara.

Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya taba fada a baya cewar zai so ya maye gurbin Del Bosque a matsayin kociyan Spaniya.