'Arsenal za ta iya lashe gasar Premier'

Image caption Cech ya ce za su bada mamaki

Golan Arsenal, Petr Cech ya ce kungiyar za ta iya lashe gasar Premier a kakar wasa ta bana.

A yanzu haka dai, maki biyu ne ya raba Arsenal da Leicester City wacce ke jan ragama a gasar.

"Wannan tawagar na da karfi kuma kocinmu zai iya saka duk dan wasan da yake so," in ji Cech.

Ya kara da cewar "Muna da babbar dama mu kai har zuwa inda ake so."

Arsenal wacce ke rike da kofin FA, a kakar wasan da ta wuce ita ce ta uku a kan tebur kuma tun a shekarar 2004 rabon da ta lashe kofin Premier.