Van Gaal ya fice daga ganawa da 'yan jaridu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester United za ta kara da Stoke a ranar Asabar

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal ya fice daga ganawa da ya ke yi da 'yan jaridu kan karawar da United za ta yi da Stoke a ranar Asabar.

Van Gaal ya fusata kan tambayar da aka yi masa kan makomarsa a United bayan da a ke rade-radin za a sallame shi daga aikin da ya ke yi.

Kociyan ya amsa tambayoyi uku ne daga 'yan jaridu kafin ya fice daga dakin ganawar kan wasan Premier da za a buga na mako na 18 a karshen sati.

Van Gaal ya ce ya halarci dakin ganawar ne saboda dokar gasar Premier da ta umarci yin hakan.

Kuma a lokacin da zai bar dakin taron ya yi wa 'yan jaridar fatan yin bikin kirsimeti lafiya, kuma ya kara da fatan shiga sabuwar shekara lafiya, wanda ya ce idan har watakila sun sake saduwa.