Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

5:18 Wannan dambe ne da aka yi tsakanin Ashiru Horo sarkin dambe daga Arewa da Mai Caji daga Kudu.

A wannan takawar Mai Caji ne ya doke Ashiru horo a damben da suka yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

5:12 Tyson Fury ya nemi afuwar kalaman da ya yi.

Hakkin mallakar hoto PA

Zakaran damben boksin ajin babban nauyi Tyson Fury ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi.

Kusan mutane dubu 140,000 ne suka saka hannu kan a zare sunan Fury daga cikin 'yan takarar da za a bai wa kyuatar dan wasan da ya fi yin fice a shekarar 2015 wadda BBC ke bayar wa a duk shekara.

Fury wanda ya lashe kambun duniya bayan da ya doke Wladimir Klitschko, ya yi jawabai ne a kan mata da 'yan luwadi wanda hakan ya harzuka mutane da dama.

Andy Murray ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi yin hazaka a shekarar 2015 da BBC ta karrama shi. Fury na biyar ya yi a zaben.

2:17 Labaran da wasu jaridun Turai suka wallafa

Hakkin mallakar hoto Daily Mirror

Daily Mirror ta wallafa cewa Leicester City na daf da kulla yarjejeniyar bai wa Jarmie Vardy fam dubu 80,000 a duk mako domin ya ci gaba da zama a kungiyar a kuma hana Chelsea wadda take kokarin sayo dan kwallon.

The Sun kuwa ta ce kociyan Arsenal, Arsene Wenger, na shirin sayo dan wasan Sevilla mai taka leda daga tsakiya Grzegorz Krychowiak mai shekara 25 kan kudi fam miliyan 33 a watan Janairu idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula.

Liverpool Echo kuwa ta wallafa cewar kociyan Liverpool, Jurgen Kloop ya tattauna da Christian Benteke domin bashi kwarin gwiwa ya dinga ci wa kungiyar kwallaye.

1:52 Wannan ne karon farko da Wayne Rooney ya zauna a benci a gasar Premier ko kuma ta zakarun Turai a wasan Manchester United tun ranar 28 ga watan Janairun 2014.

Hakkin mallakar hoto Getty

A karawar da Norwich City ta ci Man United 2-1 a gasar Premier wasan saki na 17 da suka kara a makon jiya ne Rooney ya buga wa United wasa na 500.

1:41 Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Muh'd Tasi'u Abdullahi: Gaskiya Man City za su yi duk abinda za su yi dan ganin sunci wasan su na yau ganin yadda teburi ya fara yi musu nisa, amma duk da hakan bazan fa sa adawa da su ba a yau din up gunners

Umar Bello Modibbo Wurobiriji: Wasa tsakanin Man City da Sundurland muna fatan za'a tashi lafiya. Allah ya bai wa mai rabo sa'a. Up ManUnited

Rabi'u Nuhu Nabukka: Fadan da babu ruwan ka ya fi dadin kallo, saboda haka duk yadda ta kaya dai dai. Up Barcelona

Ali M Bulama Damasak: A gaskiya karawar da za'a yi tsakanin Manchester City da Sunderland sai dai muce Allah ya bai wa mai rabo sa'a.Up Barca daga Ali M. Bulama Damasak dan Nigeria mazauni a yankin diffa a jamhoriyar Nijar.

Emmanuel Enoch Dwachem: Fatana shi ne a lallasa Man City da Man United da Totthenham, amma Arsenal da Chelsea suyi nasara.. UP GUNNERS.

1:02 Stoke City vs Manchester United

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yan wasan Stoke City: 01 Butland08 Johnson17 Shawcross26 Wollscheid03 Pieters20 Cameron06 Whelan22 Shaqiri14 Afellay10 Arnautovic27 Krkic

Masu jiran kar-ta-kwana: 11 Joselu12 Wilson15 Van Ginkel16 Adam18 Diouf19 Walters29 Haugaard

'Yan wasan Manchester United: 01 de Gea04 Jones12 Smalling17 Blind18 Young16 Carrick21 Herrera08 Mata27 Fellaini07 Depay09 Martial

Masu jiran kar-ta-kwana: 10 Rooney20 Romero28 Schneiderlin30 Varela33 McNair43 Borthwick-Jackson44 Pereira

Alkalin wasa: Kevin Friend

12:43 Belgium Jupiler League wasannin mako na 21

 • 2:30 Kortrijk vs Club Brugge KV
 • 6:00 Royal Charleroi SC vs KRC Genk
 • 8:00 Waasland-Beveren vs KSC Lokeren
 • 8:00 KV Mechelen vs KAA Gent
 • 8:30 Sint-Truidense VV vs OH Leuven

SPOR TOTO SUPER LİG Turkiya wasannin mako na 17

 • 1:00 Caykur Rizespor vs Medipol Basaksehir
 • 3:30 Antalyaspor vs Gaziantepspor
 • 6:00 Kasimpasa SK vs Trabzonspor

Scotland Premier League wasannin mako na 20

 • 4:00 Aberdeen vs Inverness C.T.F.C
 • 4:00 Hamilton vs Kilmarnock
 • 4:00 Partick Thistle vs St. Johnstone
 • 4:00 Ross County vs Dundee F C

English League Div. 1 wasannin mako na 23

 • 2:00 Brentford vs Brighton & Hove Albion
 • 4:00 Bristol City FC vs Charlton Athletic FC
 • 4:00 Derby County FC vs Fulham FC
 • 4:00 Huddersfield Town vs Preston North End
 • 4:00 Hull City vs Burnley FC
 • 4:00 Ipswich Town FC vs Queens Park Rangers
 • 4:00 Milton Keynes Dons FC vs Cardiff City
 • 4:00 Rotherham United vs Bolton Wanderers
 • 4:00 Sheffield Wednesday FC vs Birmingham City FC
 • 6:15 Wolverhampton Wanderers FC vs Reading FC

Wales Premier League wasannin mako na 20

 • 3:30 Connah's Quay Nomads vs Airbus UK Broughton
 • 3:30 Port Talbot vs Carmarthen
 • 3:30 Newtown vs The New Saints FC
 • 3:30 Haverfordwest County vs Aberystwyth
 • 3:30 Rhyl FC vs Bala Town
 • 3:30 Llandudno vs Clwb Droed Dinas Bangor

12:31 A shirinmu na sharhi da bayanan gasar cin kofin Premier, wannan makon za mu kawo muku wasan sati na 18 a karawar da za a yi tsakanin Manchester City da Sunderland.

Hakkin mallakar hoto Getty

Za mu fara gabatar da shirin da karfe 3:30 agogon Nigeria da Nijar. Za kuma ku iya bayar da gudunmawarku a BBC Hausa Facebook ko kuma ta Google+.

12:21 English Premier League wasannin mako na 18

 • 1:45 Stoke City FC vs Manchester United
 • 4:00 Liverpool vs Leicester City
 • 4:00 Tottenham Hotspur vs Norwich City
 • 4:00 Swansea City vs West Bromwich Albion FC
 • 4:00 Manchester City vs Sunderland
 • 4:00 Chelsea FC vs Watford
 • 4:00 Bournemouth FC vs Crystal Palace FC
 • 4:00 Aston Villa vs West Ham United
 • 6:30 Newcastle United FC vs Everton FC
 • 8:45 Southampton FC vs Arsenal FC