United: 'Dole mu sauya salo'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Van Gaal ya yi fushi a taron manema labarai

Kocin Manchester United, Louis van Gaal ya ce dole ne sai sun canza salonsu domin taka rawar gani a gasar Premier.

United na fuskantar matsin lamba, bayan da kungiyar ta buga wasanni shida ba tare da ta samu nasara ba, sannan kuma aka doke su sau uku a jere.

Wannan rashin nasara, shi ne mafi muni tun lokacin da Van Gaal ya soma jan ragama a Old Trafford.

"Babu tantama muna cikin yanayi mara dadi, dole sai mun canza salo," in ji Van Gaal.

A yanzu haka ana alankanta Jose Mourinho da koma wa Old Trafford din bayan da Chelsea ta kore shi.