Barcelona ya yi cinikin Guardiola ya warware

Image caption Kulab din Barcelona na Spaniya

Kulab din kwallon kafa na Barcelona na kasar Spaniya ya sayi dan wasa mai suna Sergi Guardiola, ya kuma warware cinikin, duka a rana daya!

Dan wasan dai mai goyon bayan kulab din Real Madrid ne, wato babban abokin hamayyar Bercelona, kuma cinikinsa ya warware ne bayan wasu magoya bayan Bercelonan sun bankado wasu kalaman batanci da ya taba yi a kan Barcelona da Catalonia, a shafinsa na Twitter, inda ya yi amfani da wasu munanan lafuzza cikin shekaru biyun da suka wuce.

Kulab din Barcelona na samun wannan labarin bai tsaya wata-wata ba, sai ya warware ciniki, ya ce wa Guardiola ya yi gaba.