Bolasie da Wickham za su yi jinya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bolasie dan kwallon Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Crystal Palace za ta yi rashin 'yan wasanta, Yannick Bolasie da kuma Connor Wickham na tsawon wata guda saboda rauni.

'Yan kwallon sun ji rauni ne a wasansu da Bournemouth.

Bolasie ya ji ciwo tun kafin a soma wasan gadan-gadan, a yayin da Wickham ya ji targade a kafarsa bayan ya ci kwallo a wasansu da Stoke.

"Ba za su buga wasanmu da Swansea ba. Za su yi jinyar makonni hudu,"in ji Alan Pardew.

A yanzu dai Crystal Palace ke matakin na biyar a kan tebur da maki 30 cikin wasanni 18.