Arsenal na zawarcin Elneny daga FC Basel

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mohamed Elneny na son ya koma Ingila

Arsenal ta soma tattaunawa da kungiyar FC Basel ta Switzerland domin sayen dan kasar Masar, Mohamed Elneny.

Dan shekaru 23, wanda yake murza leda a kulob din tun a shekarar 2013, ya lashe kofuna uku na gasar Switzerland.

Ana tunanin cewa darajar dan kwallon za ta kai fan miliyan biyar.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger na son ya kara karfin tawagarsa a tsakiya bayan da 'yan wasansa Francis Coquelin da Santi Cazorla da kuma Jack Wilshere ke fama da rauni.