Jakonovic ya zama sabon kocin Fulham

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fulham na fatan Jokanovic zai kai su ga nasara

Fulham ta nada Slavisa Jokanovic a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallonta.

Kungiyar ba tada koci tun da ta kori Kit Symons, a farkon watan Nuwamba.

Jokanovic, mai shekaru 47, shi ne ya tsallakar da Watford zuwa gasar Premier daga gasar Championship kafin su raba gari.

Shi ne mutum na farko da ya jagoranci kungiyar Maccabi Tel Aviv ta kai gasar zagayen farko a gasar zakarun Turai.

Kafin ya koma Fulham, sai da Fulham din ta bai wa Maccabi kusan fan dubu 370.