Messi zai buga wasansa na 500 a Barca

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Messi da Suarez da Neymar suna haskakawa a Barca

Lionel Messi zai buga wa Barcelona wasa a karo na 500, a yayin da za su fafata da Real Betis a ranar Laraba a gasar La Liga.

Messi mai shekaru 28, ya koma Spain a cikin jirginsa, bayan da ya halarci bikin da aka ba shi kyauta a Dubai.

'Yan wasan Barcelona sun yi hutu tun daga ranar 20 ga wannan watan, bayan da suka lashe kofin gasar zakarun kulob ta duniya.

"Muna son mu samu maki uku a wannan wasan," in ji kocin Barca Luis Enrique.

A wannan shekarar, Barcelona ta lashe kofuna hudu ciki har da na zakarun Turai da La Liga da kuma Copa del Rey.