Kompany zai yi jinyar makonni hudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kompany bai buga wasan lig-lig 11 cikin 19 da City ta fafata a bana ba.

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce kyaftin din kungiyar, Vincent Kompany, zai yi jinyar makonni uku zuwa hudu sakamakon raunin da ya yi a kaurinsa.

Kompany, mai shekara 28, ya yi ta dingishi a lokacin wasan da suka doke Sunderland washe garin ranar Kirsimeti.

A ranar Talata, City ta tashi 0-0 a wasan da ta yi da Leicester, kuma shi ne karon farko a kakar wasannin Premier ta bana da suka yi wasa ba tare da Kompany ba.

Pellegrini ya ce dan wasan ya ji rauni ne a "kaurin da ya saba jin rauni, ko da ya ke ba a gefen da ya saba jin rauni ba."

City dai na matsayi na uku a saman teburin Gasar Premier.

Kompany bai buga wasan lig-lig 11 cikin 19 da kungiyar ta fafata a bana ba, sakamakon raunin da ya yi a kaurinsa a wasan da suka yi da Juventus ranar 15 ga watan Satumba.

Ya koma buga wasa na 'yan wasu kwanaki a karshen watan Oktoba, sai dai bai sake yin wasa ba sai wanda City ta doke Sunderland da ci 4-1 .

Ko da a wasan nasu, bai wuce minti tara yana murza leda ba kafin a cire shi.