Barcelona ta kafa sabon tarihi a Spain

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona na ci gaba da haskakawa a duniya

Barcelona ta kafa sabon tarihin a gasar kwallon kafa a Spain, inda ta zura kwallaye 180 a shekarar 2015.

Kenan Barcelona ta shiga gaban Real Madrid wacce a shekarar 2014 ta zura kwallaye 178.

Bajintar da Barcelona ta kafa, ya biyo bayan doke Real Betis ne da ci hudu da daya, inda Messi da Suárez suka ci kwallaye.

Lionel Messi wanda wasan ya kasance na 500 da ya bugawa Barcelona, ya tabbar da cewa kungiyarsa ta ci gaba da jagorancin teburin gasar La Liga a yayin da shekarar ke karewa.

A wannan shekarar, Barcelona ta lashe kofuna hudu ciki har da na zakarun Turai da La Liga da Copa del Rey da kuma na zakarun kungiyoyi na duniya.