Fifa: Bility ya kara gamuwa da cikas

Hakkin mallakar hoto
Image caption Fifa ta ce Bility ba zai iya takarar shugabanci ba

Shugaban hukumar kwallon Liberia, Musa Bility ya yi rashin nasara wajen kalubalantar hana shi takarar shugabancin Fifa.

A ranar 12 ga watan Nuwamba ne, Fifa ta ce Bility bai 'dace' ya tsaya takara ba.

Sai ya daukaka kara zuwa kotun sauraron kararrakin wasanni (Cas), domin ganin an bar shi ya yi takarar.

Amma a ranar Alhamis, wata sanarwar kotun Cas ta ce "An kori karar da aka shigar."

"Na ji mamakin wannan hukuncin," in ji Bility.