Manchester United ta doke Swansea da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier

Manchester United ta doke Swansea da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 20 da suka yi a filin wasa na Old Trafford a ranar Lahadi.

Anthony Martial ne ya fara ci wa United kwallo, kuma Gylfi Sigurdsson ya farkewa Swansea kwallon da aka zura mata, daga baya Rooney ya ci wa United kwallo ta biyu.

Da wannan sakamakon United ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier, inda Swansea kuwa ke matsayi na 17 da maki 19.

United za ta buga wasan Premier na gaba da Newcastle United, inda Swansea za ta karbi bakuncin Sunderland a wasan mako na 21 na gasar.